Ivory Coast: An yi na'am da gyara kundin tsarin mulkin kasar

Alassane Ouattara ya ce za a samu ci gaba a kasar idan akayi garanbawul a kundin tsarin mulkin kasar
Bayanan hoto,

Alassane Ouattara ya ce za a samu ci gaba a kasar idan akayi garanbawul a kundin tsarin mulkin kasar

Hukumomi a Ivory Coast sun bayyana cewa al'umar kasar sun yi na'am da sauya-sauyen da shugaba Alassane Ouattara ya gabatar a kundin tsarin mulkin kasar a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kada a ranar Lahadi.

Jami'ai sun ce kashi 99 cikin 100 na wadanda suka kada kuri'ar su na goyon bayan matakin da gwamnatin ta dauka kuma kashi 40 cikin 100 na wadanda suka ka isa kada kuri'a ne suka fito.

Wakilin BBC yace 'yan adawa sun ce kashi 10 cikin 100 na mutanen kasar ne kadai suka kada kuri'a.

Sai dai duk da hakan shugaba Alassne Ouattara shi zai yi nasarar sauya sabon kundin tsarin mulkin kasar da zai kara masa karfin iko.

Shugaba Alassane Ouattara ya ce kuri'ar raba gardama zata taimakawa kasar wajen samun ci gaba bayan shekarun da aka shafe ana fama da rikici.