Wani Yarima ya sha bulala a Saudiyya

Jama'a a Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kawo yanzu ba a bayyana wannan labari a hukumance ba

Rahotanni sun ce mahukunta a Saudiyya sun zane wani Yariman gidan sarautar kasar bayan da aka same shi da aikata laifi.

Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da aka kashe wani jinin sarautar kasar bisa laifin kisan kai.

Amma kawo yanzu ba a bayyana suna ko ainahin laifin da yariman ya aikata ba.

Sai dai ba kasafai ake samun jinin gidan sarautar da laifi ba ko kuma a yanke musu irin wannan hukunci.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta a kasar sun yi farin ciki da hukuncin, suna masu cewa ya nuna yadda shari'ar Musulunci ke bi ta kan kowa.

Kawo yanzu ba a bayyana wannan labari a hukumance ba.