Nigeria: Hotunan bikin baje kolin hotuna a birnin Lagos

Bikin baje kolin hotunan da aka yi a Najeriya ya hada sanan nun masu daukar hoto, wadanda suka nuna yadda suke kallon asalin nahiyar Afirka.

Bikin "Royal Generation" da ke nuna yadda mata ke sanye da tufafin al'ada, wanda 'yar Angola Keyezua, wadda ke aikin baje kolin tufafi ta shirya

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Keyezua na kwalliya a kasar Angola da irin wannan tufafi, wanda aka yi wa lakabi da 'Royal Generation' watau 'Sarautar zamani', inda mace ke sanya kayan da aka hada da kayan sarrafawa na karkashin kasa.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Jerin hotunan mutane da dan Ghana Eric Gyamfi, mai daukar hoto ya hada, domin nuna suffar maza.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Mai daukar hoto dan Najeriya, Lakin Ogunbanwo ya yi nazari kan al'ada da kuma zamani, inda ya hada kayan zamani da na gargajiya.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Tawakkali shi ne mafita ga duk kunci, wannan shi ne maudu'in da mai daukar hoto TSoku Maela, dan asalin Afirka ta Kudu ya kirkiro, yana mai cewa, "Ka so kanka domin kawo ingantacciyar sauyi ga rayuwar ka".

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Mai daukan hoto Osborne Macharia, dan asalin Kenya, ya yi nazari kan kamannin tsoffin mata da suka yi ritaya da yadda za su fito a wani shiri mai suna Nyanye - watau tawagar kakanni masu almubazzaranci.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Mai daukar hoto dan kasar Benin Ishola Akpo, ya dauki hoton kakarsa, cikin jerin hotunan da ya hada domin nuna muhimmancin sadaki a al'adar Afirka.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Wannan hoton na cikin jerin hotunan da aka yi wa lakabi da Genesis, wanda Kudzanai Chiurai ya dauka, winda ya duba yanayin siyasa da harkokin al'ummar Zimbabwe, kuma ya yi kokarin gane yanayin tunaninsu a lokacin mulkin mallaka.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Aikin Adad Hannah's kenan mai suna 'The Raft of the Medusa', sakewar wani hoto na karni na 19 da Theodore Gericault ya yi, wanda hoto ne da aka dauka na wani jirgin ruwa da ya lalace a Senegal fiye da shekara 200 da suka gabata.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Basirar tsira da ranka watau 'The Art of Survival' da mai daukar hoto Patrick Willocq, dan asalin Faransa ya yi, wanda ya zauna a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a baya, inda ya fito da yadda rayuwa ta ke kasance wa yara 'yan gudun hijira, yana bayar da labari cikin zane.

Asalin hoton, Lagos Photo Festival

Bayanan hoto,

Wannan hoto mai suna 'Profit Corner' aikin dan Mozambique ne Mario Macilau mai daukar hoto, inda ya nuna yadda dattin lataroni ke barazana ga al'ummar Afirka.

Hotunan da aka dauka yayin bikin baje kolin hotuna da ake yi a jihar Lagos da ke Najeriya, wanda za a yi har ranar 22 ga watan Nuwambar 2016.