Golar Gambia ta nutse a ruwa a hanyar shiga Turai

Migrants in a boat

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fiye da 'yan cirani da 'yan gudun hijira 3,300 suka mutu a tekun Bahar-rum a bana

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafar mata ta kasar Gambiya ta mutu bayan ta nutse a ruwa a tekun Bahar-rum lokacin da ta ke kokarin shiga nahiyar Turai.

Hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce Fatim Jawara, mai shekara 19, tana cikin wani kwale-kwale ne da ya samu matsala a watan da ya gabata.

Shugaban hukumar Lamin Baba ya shaida wa BBC cewa dangin Fatim sun tabbatar da mutuwarta.

Da dama daga cikin 'yan ciranin da ke tsallaka wa Italiya sun fito ne daga Gambia.

Jawara ta fara buga wa kasar kwallo ne a bara, bayan da ta taka leda a tawagar matasa ta Gambia.

Mista Bajo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Za a iya tuna ta saboda fanaretin da ta kade a wasan sada zumunta tsakanin kasar da kuma Glasgow Girls na Scotland".

Fiye da 'yan cirani da 'yan gudun hijira 3,300 ne suka mutu a tekun Bahar-rum a bana.

Asalin hoton, Jennifer O'Mahony/@Twitter

Bayanan hoto,

Mahukunta a Gambia sun ce za a tuna Fatim da irin rawar da ta taka a fagen kwallo