IS: Za mu ci gaba da gwawarmaya a Mosul

Yadda ake luguden wuta dan karbe birnin Mosul daga hannun 'yan IS

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mayakan IS sun kai shekaru biyu da karbe iko da birnin Mosul

Kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS ta fitar da wani sakon murya da ta yi ikirarin muryar shugaban kungiyar ne Abu Bakr al-Baghdadi.

A cikin muryar ya yi kiran magoya bayansu kada su karaya su ci gaba da fafutuka don kare birnin Mosul daga hannun dakarun gwamnatin Iraqi da na kawance.

Ya kuma ce babu gudu ba ja da baya don haka ya na da kwarin gwiwar nasara na tare da su.

Wannan dai shi ne karon farko da Al-Baghdadi ke aiko da irin wannan murya cikin shekara guda, hakan kuma na zuwa ne makwanni biyu da gwamnatin Iraqi ta kaddamar da hare-hare babu kakkautawa dan fatattakar masu kaifin kishin Islamar daga cikin birnin.

Hukumar kare hakin bil'adam ta Amnesty International ta ce alamu sun nuna cewa an samu karuwar kai hare-hare kan mutanen dake birnin da kuma tursasawa yara kanana marawa mayakan na IS baya.

Wakilin BBC ya ce zargin da Amnesty ta yi a cikin rahotonta ya shafi mayakan Sunni ne na kabilu masu fada aji a Iraqi, kuma ana kai hari kan duk wanda ya ke da alaka da mayakan IS a kauyukan da aka kame da ke kudu maso gabashin birnin Mosul.