Ghana: Hukumar zabe ta rufe shafinta na intanet

Asalin hoton, Getty Images
Nan da makonni kusan biyar ne za a yi babban zaben kasar Ghana
Rahotani daga Ghana na cewa an rufe shafin intanet na hukumar zabe da kasar, yayin da ya rage kusan makonni biyar a yi babban zaben kasar.
Da farko dai wasu sun dauka cewa ko masu satar shiga shafukan intanet ne suka shiga shafin, sai dai hukumar ta ce na'urar intanet din ce ta samu matsala kuma ana kokarin gyarawa.
Wasu 'yan kasar dai na ganin cewa akwai lauje cikin nadi kan wannan hukunci da hukumar zabe ta dauka.
A baya dai duk wasu bayanai da ake bukata da suka shafi shirye-shiryen zaben da ma lokutan zaben a shafin na hukumar zabe ake samu.
Dan haka sun yi kira da a dauki matakin gaggawa na gyara shafin internet din na hukumar zaben Ghana, dan saukakawa jama'a sanin halin da ake ciki a kasar.