Rasha: 'Yan IS su fice daga Aleppo cikin kwana 2

Yadda yakin shekaru 5 ya daidaita birnin Aleppo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yakin basasar da Syria ke ciki ya janyo miliyoyin 'yan kasar sun yi gudun hijira zuwa kasashe makofta kamar Lamanun

Dakarun kasashen Rasha da Syria sun shaidawa mayakan 'yan tawaye da ke birnin Aleppo cewa sun ba su yau zuwa gobe juma'a su fice daga birnin.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta rawaito cewa za su baiwa 'yan tawaye damar ficewa daga Alepppo ba tare da ko kwarzane ba, za kuma su samu damar wucewa tare da kayan yakin su amma ta hanyoyi biyu da aka amince su wuce ta nan.

Ya yin da za a bude wasu hanyoyi shida da fararen hula da marasa lafiya da tsofaffi da yara har ma da mata wanda suka makale a cikin birnin na Aleppo za su fice.