Duniya za ta shiga-uku idan aka zabi Trump - Obama

Asalin hoton, Reuters
Obama ya ce Trump hatsari ne ga duniya
Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga 'yan jam'iyyar Democrats daga kowacce kabila su fito su zabi Hillary Clinton, yana mai gargadin cewa 'yan Republic da ma sauran al'umar duniya za su shiga uku idan Donald Trump ya zama shugaban kasar.
Obama ya ce Trump hatsari ne ga 'yancin kasar na walwala.
Shugaban na Amurka na magana ne a wajen yakin neman zaben Hillary Clinton jihar North Carolina.
Sai dai Mr Trump ya ce ya kamata Mr Obama ya daina yi wa Clinton yakin neman zabe, ya mayar da hankali kan mulkin kasar.
Ya shaida wa magoya bayansa a Pensacola da ke Florida cewa,"Babban batu dai shi ne babu wanda ke son Obama ya sake mulki tsawon shekara hudu."
Ya ce a 'yan kwanakin nan Mrs Clinton ta zama "mahaukaciya."
A ranar Talatan makon gobe ne dai Amurkawa za su kada kuri'unsu a zaben da ke cike da ce-ce-ku-ce, yayin da kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa 'yan takarar biyu sun yi kankankan.