Mun ji kunya da aka doke mu a gida - Pochettino

Tottenham ta sha kashi sau shida a Wembley

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tottenham ta sha kashi sau shida a Wembley

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce ba wasan da suka yi a Wembley ba ne ya sa suka sha kashi a hannun Bayer Leverkusen a gasar cin kofin zakarun turai.

Bayer Leverkusen ta doke Tottenham da ci 1-0 ranar Laraba kuma hakan na nufin sun sha kashi a dukkan wasannin cin kofin turai a gida a bana.

Pochettino ya ce: "Babu inda ba a samun matsala a kwallon kafa a duk duniya. Matsalar a wurinmu take ba a Wembley ba."

Tottenham na da zabi ta buga dukkan wasannin lig na gida da kuma na cin kofin turai a Wembley a kakar wasa mai zuwa.

Pochettino ya kara da cewa: "Wannan lamari babban abin kunya ne a gare ni. Ba mu da wani katabus ganin cewa mun yi wasa biyu a Wembley, inda Monaco da Bayer Leverkusen, suka kayar da mu. Laifin a wurinmu yake."