Yaya zurfin ilimin shuagabannin duniya?
Akalla kashi 80% cikin dari na shugabanni na da ilimin boko, da suka fi mayar da hankali kan tattalin arziki da kuma tsarin shari'a
Shugabannin duniya goma sha bakwai ne suka mayar da hankali kan wasu fannoni na ilimin soja, inda hudu daga cikin su suka yi makarantar sojoji na Royal Military Academy da ke Sandhurst.
Amma kuma rashin karatun boko, bai hana Jacob Zuma zamowa shugaban kasar Afrika Ta Kudu ba.