An yi zanga-zanga kan gwamnan da ya yi 'saɓo' a Indonesia

Asalin hoton, AFP
Purnama shi ne dan kabilar China na farko da ya zama gwamna
Dubban Musulmi ne suke yin zanga-zanga a Indonesia, inda suke kira a hukunta gwamnan birnin Jakarta saboda ya yi sabo.
Basuki Tjahja Purnama, wanda Kirista ne, shi ne dan kabilar China na farko da ya zama gwamna a kasar da mafi yawan mutanenta Musulmi ne.
Masu zanga-zangar sun taru a Masallacin Istiqlal kuma daga nan suka nufi fadar shugaban kasar.
'Yan sanda sun daura damara domin tunkarar yiwuwar barkewar rikicin addini.
A shekarar 1998, an yi zanga-zangar kin jinin 'yan China lamarin da ya kai ga kona kantuna da gidaje da kuma sace kayayyakin 'yansu.
'Yan kabilar China su ne kusan kashi daya cikin dari na al'umar Indonesia kimanin 250m.
Mr Purnama, wanda aka fi sani da "Ahok", na shirin sake tsayawa takara a watan Fabrairu na shekarar 2017.
Sai dai wasu Musulmi sun ce bai kamata ya tsaya ba, suna masu cewa bai kamata wanda ba Musulmi ba ya jagoranci Musulmi.
Sun kara da cewa bai kamata ya rika amfani da ayoyin Al-Qur'ani wajen yakin neman zabe ba.