Mourinho ya caccaki 'yan wasan Manchester United

Mourinho ya ce 'yan wasan ba su da himma

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mourinho ya ce 'yan wasan ba su da himma

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya zargi 'yan wasansa da yin wasa irin na "sada zumunta" bayan sun sha kashi a hannun Fenerbahce.

United ta fadi zuwa mataki na uku a rukunin A na gasar cin kofin Europa bayan Fenerbahce ta doke su da ci 2-1 a Istanbul.

Yanzu dai kungiyar ta lashe wasa biyu ne kawai cikin wasanni bakwai da ta buga na dukkan gasar da take ciki.

Mourinho ya ce, "duk kungiyar da aka ci wasa bayan minti biyu da shiga fili ba a shirye take ba, kuma ba ta da alkibla".

United ta ci kwallaye biyu kawai a wasanni hudu na baya-bayan nan da ta buga, yayin da Chelsea ta zura mata kwallo dakika 30 da soma wasa, kuma Fenerbahce ta ci ta a dakika 65 na farko.

Moussa Sow ya fara zura kwallo, yayin da Jeremain Lens ya kara ta biyu daga bangaren Fenerbahce, kafin Wayne Rooney ya ci wa United tata kwallon daga bisani.