Toure ya bayar da kai bori ya hau

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pep Guardiola ya caccaki Toure

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure ya nemi gafarar kungiyar "saboda abubuwan da suka faru a baya".

Kocin City Pep Guardiola ya ce ba zai sanya Toure, mai shekara 33 a wasa ba, sai lokacin da wakilinsa Dimitri Seluk ya nemi gafara a kan sukar da ya yi masa saboda kin sanya dan kwallon a jerin 'yan wasan da ke buga gasar zakarun turai.

Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Toure, ya ce "Ina neman gafara - a madadi na da wadanda ke wakilta ta."

Ya kara da cewa "Ba a fahimci kalaman da aka yi ba, don haka ba sa nuna akwai matsala tsakanina da kulob dina."

Seluk ya ce an wulakanta Toure saboda rashin sanya shi a cikin tawagar da ta buga gasar zakarun turai.

Shi kuma kocin City ya ce: "Ba zan lamunci yanayin da dan wasa zai caccake ni a kafafen watsa labarai ba saboda ban sanya shi a wasa ba."

Toure, wanda bai buga wa City wasa ba tun ranar 24 ga watan Agusta, ya kara da cewa : "Ina matukar mutunta Manchester City kuma ina yi wa kulob din fatan alheri."

Ya kara da cewa: "Ina matukar alfahari da na buga wa kulob din wasa kuma ina son taimakon sa domin ya ci gaba da yin nasara. Zan ci gaba da buga kwallo domin na burge 'yan kallo."