Masu kutse sun katse intanet a Liberia

Masu kutse sun yi nasara
Bayanan hoto,

Masu kutse sun hana Liberia sakat

A lokuta da dama masu kutse sun yi ta katse hanyoyin samun intanet a Liberia inda suka rufe hanya daya tilo da kasar ke samun intanet din.

Hare-haren da suka rika kai wa wayar da ke samar da intanet din ga kasar a ranar uku ga watan Nuwamba sun sa intanet din ta rika katsewa.

Masu bincike sun ce hare-haren sun nuna cewa masu kutsen sun rika kokarin yin amfani da hanyoyi da dama na satar bayanai daga wuraren sirri.

Masana sun ce gungun masu kutsen ne ya taba yin kutsen da taba durkusar da hanyoyion intanet a kasar ranar 21 ga watan Oktoba.

Hare-haren na daha cikin manya-manyan kutsen da suka hana samun intanet din manyan shafukan intanet irin su Twitter, Spotify da kuma Reddit.

Hare-haren na cikin wadanda aka fi yin amfani da su wajen yada kwayoyin cutukan kwamputa ga na'urorin da ba su da kariya sosai.