Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka idan Trump ya ci zabe

Wole Soyinka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A matsayin shi na shahararren marubuci, ba lallai bane Wole Soyinka ya fuskanci matsala wajen samun katin green card

Shahararren marubucin nan na Najeriya, Wole Soyinka, ya ce zai yaga katinsa na shaidar zama a Amurka wanda ake kira green card, idan har Donal Trump ya ci zabe.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa Mista Soyinka na cewa ba lallai ba ne Trump ya ci zaben, a lokacin da yake jawabi a jami'ar Oxford da ke Birtaniya.

Ya kara da cewa amma kuma idan har ya ci, to abu na farko da zai fada shi ne "duk masu katin shaidar zama a Amurka na green card sai sun sake neman izini".

Jaridar ta ambato shi yana cewa "to ni ba zan jira wannan ba".

Ya kara da cewa "Da zarar sun sanar da nasarar shi, zan yaga kati na da kai na, sannan na fara tattara kayana".

Mista Soyinka dai malami ne a cibiyar nazari kan harkokin Afirka da Amurka da ke jami'ar New York.

Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu lambar yabo na Nobel a kan rubutun adabi a shekarar 1986.