Nigeria: Mutum 700,000 na neman guraben aiki 500

Matasa a nahiyar Afirka na fama da rashin aikin yi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Matasa a Najeriya na fama da rashin aikin yi duk da arzikin man da kasar ke da shi

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu fiye da masu neman aiki dubu 700 da ke neman guraben aikin da aka tallata na mutum 500 a hukumar tara haraji ta kasar, FIRS.

Shugaban Hukumar Tunde Fowler ne ya bayyana hakan ga kwamitin majalisar wakilan kasar kan sauraron koke-koken jama'a.

Ya ce sama da mutum 2, 000 daga cikin masu neman aikin na da digiri daraja ta daya, kuma dukkansu sun cancanci a dauke su.

Hakan na zuwa ne a yayin da kasar ke cigaba da fama da matsalar tatattalin arziki mafi muni cikin shekaru.

Wannan lamari dai ya nuna yadda ake fama da rashin aikin yi a Najeriya, kasar da ta fi kowacce girman tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a turmutsutsun neman aiki shekara biyu da ta wuce a sassan kasar daban-daban.

Matasa a Najeriya dai na cigaba da fama da rashin ayyuka, wanda hakan ke da matukar barzana ga zaman lafiyar kasar baki daya.

Masu sharhi na ganin rashin abun hannu na daya daga cikin dalilan da rikice-rikice kamar na Boko Haram da mayakan Naija-Delta ke cigaba da ruruwa.