Nigeria: Sayen kayan daki ya gagari wasu iyaye a Kano

Bayanan sauti

Kafintoci sun koka a Kano

Wasu iyaye a Nigeria sun ce sun kasa saya wa 'ya'yensu mata kayan daki saboda tsadar rayuwar da ake fama da ita.

A kasar Hausa iyayen budurwa ne kan saya wa 'yarsu kayan daki da suka hada da gado da kujeru kafin tarewa a gidan aurenta.

Sai dai, a baya-bayan nan, matsin tattalin arziki da ake fuskanta a Najeriya ya janyo hauhawar farashi da raguwar harkokin saye da sayarwa.

Su ma kafintoci na kokawa kan karancin kasuwar da suke fuskanta saboda yawan daga bukukuwan aure, sakamakon rashin halin sayen kayan daki.

Za ku iya sauraron rahoton da wakilinmu Mukhtar Adamu Bawa ya hada mana a farkon wannan labarin.