An taso keyar 'yan Ghana 108 daga Amurka

Bayanan sauti

Amurka ta taso keyar wasu 'yan Ghana

Gwamnatin Amurka ta taso keyar wasu 'yan kasar Ghana su 108 zuwa kasarsu.

Mutanen dai sun hada da bakin-haure da wadanda suka kawo karshen zaman su a gidan kaso.

Wadansu daga cikinsu dai sun isa filin saukar jiragen saman Accra, babban birnin kasar ta Ghana, daure da ankwa da sarkoki.

Amurkar dai ta zarge su da kin ba da hadin kai ga jami'an tsaro a lokacin da aka yi kokarin kama su.

Gwamnatin Amurkar ta ce ta mayar da su Ghana ne bisa zargin su da aikata laifuffuka daban-daban, wadanda suka hada da safarar miyagun kwayoyi, da sata da fyade da damfara, da kuma fadace-fadace.

Mutanen dai sun musanta zarge-zargen, sun kuma yi korafin cewa jami'an tsaron Amurka sun muzguna masu.

Wakilinmu Iddi Ali ya aiko mana da karin bayani; sai ku saurari rahotonsa a farkon wannan labarin.