MDD ta ce mutane 239 sun mutu a tekun Bahar Rum

'Yan gudun hijira da ke kokarin tsallaka tekun Bahar Rum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hukumar ta UNHCR ta ce yawancin wadanda suka rasu 'yan kasashen Najeriya ne da Guinea

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce akalla 'yan gudun hijira 239 ne suka mutu bayan lalacewar wasu jiragen ruwa biyu a tekun Libya ranar Laraba.

An kai wadanda aka ceto daga cikin su kasar Italiya.

Hukumar ta UNHCR ta ce yawancin wadanda suka rasu 'yan kasashen Najeriya ne da Guinea.

Ana dai yi wa Bahar Rum kallon tekun da ya fi kowanne hadari wajen tsallakawa a duniya.

A bana kadai, sama da mutane 400 ne suka mutu yayin da suke kokarin tsallaka tekun zuwa kudancin Turai.

Yawanci sun fito ne daga Libya, kasar da har yanzu ke fama da tashin hankali da rashin bin doka.

A wannan makon ne Kungiyar Tarayyar Turai, EU, ta soma bayar da horo ga wadansu ma'aikatan gabar tekun Libya, a wani yunkuri na ganin an dakile tsallaka tekun mai hadari da 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani ke yawan yi.