Rasha za ta ci gaba da luguden wuta a Syria

Birnin Aleppo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yakin Syria ya raba miliyoyin 'yan kasar da muhallansu

Rasha ta sanar da cewa za ta sanya ido akan tsagaita wuta na sa'o'i goma sha biyu, dan bai wa mayaka 'yan tawaye da fararen hula da marasa lafiya damar ficewa daga birnin Aleppon Syria.

Tun da fari 'yan tawayen sun yi watsi da tayin da Rasha ta yi musu na ficewa daga birnin tsakanin jiya alhamis da yau juma'a, sun kuma ci gaba da kokarin kutsawa yankunan da gwamnatin Syria ta yi wa kawanya a gabashin gundumar birnin Aleppo.

Inda suka ci gaba da harba makaman roka da kai hare-haren kunar bakin wake da ya hallaka fararen hula da dama cikin kwanaki shida da suka gabata.

Da yammacin yau ne ake sa ran jiragen yakin Rasha da Syria za su ci gaba da luguden wuta a yankunan da 'yan tawaye suke fakewa.

Yakin basasar Syria da aka dauki shekaru biyar ana yi tun bayan juyin juya hali da guguwar sauyin da ta kada a kasashen gabas ta tsakiya, ya san an yi asarar rayukan dubban 'yan kasar, wasu muliyoyi sun rasa muhallansu, ya yin da wasu miliyoyin kuma suka tsere daga kasar.

A bangare guda kuma shugaba Basharul Assad wanda manyan aminan sa irin su Rasha ke marawa baya, ya kafe kai da fata ba zai sauka daga kujerar sa ba kamar yadda 'yan tawaye da kasashen yammacin duniya suka bukata.