Erdogan: An kama 'yan majalisa na jam'iyyar adawa

Shugaba Erdogan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba, gwamnatin Turkiyya ke daukar matakin kame duk wanda ake zargi da aikata ta'addanci

Hukumomin kasar Turkiyya sun tsare 'yan majalisar dokokin kasar goma sha daya na jam'iyyar HDP mai goyon bayan Kurdawa, ciki kuwa har da shugabansu.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sanda sun yi wa gidajen Selahattin Dermirtas da Figen Yukserkdag kawanya, a wani bangare na binciken ayyukan ta'addanci a kasar.

Wani dan majalisar dokoki Ertugrul Kurkcu ya shaida wa BBC cewa ba a bi ka'ida ba wajen kame mutanen.

A bangare guda kuma rahotannin da ke fiwowa daga birnin Santambul sun tabbatar da cewa an rufe kafafen sada zumunta na Facebook da Twitter a kasar.

A baya dai gwamnatin Turkiyya ta zargi jam'iyyar HDP da marawa haramtacciyar kungiyar 'yan ta'adda ta PKK.

A farkon wannan shekara ma shugaba Racep Tayyip Erdogan ya amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar garanbawul mai cike da cece-kuce, wanda zai ba wa gwamnati damar cirewa 'yan majalisa rigar kariya dan su fuskanci shari'a.