Gwamnatin Nigeria za ta kara wutar lantarki

Har yanzu ba ta sauya zani ba game da lantarkin Najeriya
Bayanan hoto,

Har yanzu ba ta sauya zani ba game da lantarkin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta cimma yarjejeniya da wasu hukumomi domin samar da karin megawat 500 na wutar lantarki a kasar.

Wannan yarjejeniya, kamar yadda mahukunta ke cewa, za ta taimaka wajen bude wa wasu kamfanoni ido wajen zuba-jari a bangaren samar da makamshi a kasar.

Najeriya ta ce an cimma yarjejeniyar ce da kamfanoni da kuma wasu hukumomi irin su kamfanin samar da wutar lantarki na yankin Niger-Delta, wato Niger Delta Power Holding Company, tare da agajin Bankin Duniya.

Wata sanarwar da ofishin mataimakin shugaban kasar ta fitar ta ce yarjejeniyar tana da matukar muhimmanci, saboda za ta habaka harkar samar da makamashi a kasar.

A cewar sanarwar, Kamfanin Seven Energy da ke samar da iskar gas ya dukufa wajen zuba-jarin da ya kai dala miliyon 500 don gina cibiyar sarrafa iskar gas a jihar Akwa-Ibom.

Bankin Duniya zai tsaya wa kamfanin Niger-Delta Power Holding Company a kokarin da yake yi da kamfanin Seven Energy don sarrafa iskar gas din zuwa wutar lantarki a wata cibiya da ke Calabar, babban birnin jihar Cross-River.

Najeriya dai na fama da matsalar karancin wutar lantarki, kasancewar a halin da ake ciki, wutar da take samarwa bai kai megawatt 4000 ba.

Ga ta kuma da yawan al`umar da ta kai miliyon 180, wadda masana ke cewa tana bukatar ninkin baninkin wutar da gwamnati ke samarwa yanzu, kafin a kai ga gamsar da al`umar kasar.

Gwamnatocin da suka gabata dai sun dauki matakai daban-daban da nufin inganta wutar lantarki a kasar.

Wannan ya kama daga sauya wa hukumar wutar kasar sunaye iri-iri, zuwa sayar da hannayenn-jarinta ga wasu da aka ce `yan kasuwa ne.

Amma har yanzu ba ta sauya zani ba, sakamakon zargin da ake yi na cin hanci da kuma matsalar hare-haren da `yan bindiga ke kaiwa kan bututan da ke samar da iskar gas a yankin Niger Delta.