Dan majalisa ya dauki hutu don shan maganin hauka

Ludlam

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ludlam ya samu fatan alheri

Wani dan majalisar dokokin Australia ya samu goyon baya sosai bayan da ya fito fili ya ce zai tafi hutu domin yin jinyar damuwa.

Scott Ludlam, mai shekara 46, wanda kuma mataimakin shugaban jam'iyyar Australian Greens ne, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya jima yana fama da matsalar rashin lafiya da kuma ta tabin-hankali.

Ya kara da cewa, "Zan koma bakin aiki da zarar na samu lafiyar iya ci gaba da ayyukan da ke gabana."

Sanata Ludlam ya ce,"Ina alfahari da cewa ina samun kyakkyawar kulawa daga wurin abokaina da 'yan uwana da kuma likitocina ."

Manya-manyan 'yan siyasar Australia sun yi masa fatan alheri a sakonnin da suka wallafa a shafukan sada zumunta, suna masu jinjina masa kan yadda ya fito fili ya bayyana larurar tasa.