Sojoji sun dakile wani harin kunar-bakin-wake a Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta murkushe Boko Haram

Asalin hoton, NIGERIA ARMY

Bayanan hoto,

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta murkushe Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce wani jami'inta ya harbe wata mace 'yar kunar-bakin-wake da ta yi yunkurin tayar da bam a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aikewa manema labarai, ta ce an harbe matar ne a yayin da take yunkurin shiga wani sansanin soji da ke Yamtake a karamar hukumar Gwoza.

A cewarsa, hakan ya faru ne jim kadan bayan soji sun dakile wani hari da 'yan ta'adda suka yi yunkurin kai wa.

Sanarwar ta ce sojojin sun kashe maharan guda hudu, cikinsu har da 'yan kunar-bakin-wake biyu sannan suka kwace bindigogi da alburusai da kuma miyagun kwayoyi daga wajen su.

Sai dai Kukasheka ya kara da cewa soja daya ya rasa ransa a lokacin ba-ta-kashin.

Rundunar sojin Najeriya dai ta matsa kaimi a kokarin da take yi na kawar da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane kana ta raba miliyoyi da muhallansu.