Sojoji sun sake 'ceto' wata 'yar Chibok

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sake ceto wata 'yar Chibok

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Soji sun ce an gano ta ne a lokacin da ake tantancewa

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake samun daya daga cikin matan Chibok da aka sace tun a shekarar 2014.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aikewa manema labarai ta ce an gano 'yar Chibok din ce a Pulka da ke jihar Borno lokacin da sojoji ke tantance wasu daga cikin mutanen da suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram daga dajin Sambisa.

Ya ce sunan ta Maryam Ali Maiyanga, kuma tana dauke da jariri dan wata goma mai suna Ali.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar ya ce an mika ta ga likitoci domin su duba lafiyarta.

A watan Oktoba ne dai aka saki 'yan matan Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannun kungiyar ta Boko Haram.

A wancan lokacin, kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya ce "An sako matan ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da Boko Haram sakamakon shiga tsakanin da gwamnatin Switzeland da kungiyar International Red Cross suka yi."