Ana ci gaba da kama wasu 'yan jarida a Turkiyya

Cumhuriyet na cikin tsirarun jaridun da ke sukar Mr Erdogan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Cumhuriyet na cikin tsirarun jaridun da ke sukar Mr Erdogan.

An kama 'yan jarida tara da ke aiki da jaridar 'yan hamayya ta Cumhuriyet da ke Turkiyya, kana aka tsare su a gidan yari kafin a yi musu shari'a a birnin Istanbul.

Editan jaridar da mai zayyana hotunan barkwanci da kuma wani mai rubuta sharhin da ke sukar gwamnati na cikin 'yan jaridar da aka kama.

Su ne 'yan jarida na baya bayan nan da aka kama ana zargi da sukar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ranar Juma'a, an daure 'yan siyasa tara, cikin su har da shugabannin jam'iyyar da ke goyon bayan Kurdawa ta HDP.

Haka kuma ranar Asabar an kama 'yan jam'iyyar HDP tara, cikinsu har da shugabannin yankunan da suka hada da na lardin kudu maso gabashin kasar na Adana.

Cumhuriyet na cikin tsirarun jaridun da suka rage da ke ci gaba da sukar Mr Erdogan.

Ana zargin ma'aikatanta da alaka da fitaccen Malamin nan dan kasar Fethullah Gulen da ke zaune a Amurka, wanda ake zargi da hannu a kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Yuli.