Fitaccen masanin harshen Hausa Mu'azu Sani Zaria ya rasu

Asalin hoton, BUK
Farfesa Zaria ya yaye dubban dalibai
Allah ya yi wa fitaccen masanin harshen Hausan nan na Jami'ar Bayero ta Kano da ke Najeriya, Farfesa Mu'azu Alhaji Zaria Sani rasuwa ranar Juma'a.
Farfesa M.AZ., kamar yadda aka fi saninsa, ya rasu ne a birnin na Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Masanin ya yi fice wajen ilimin sarrafa harshe da nahawun Hausa.
Ya yi karatunsa a Najeriya da Ingila.
Farfesa Mu'azu Sani Zaria ya yaye dubban dalibai da suka yi nazari kan ilimin tsarin sauti da harshen Hausa da ma Turancin Ingilishi.
Kazalika ya rubuta makaloli da littattafai da dama a fannin Hausa, cikinsu akwai:
*Karin mujtath a harshen Hausa.
*Gajeren wasalin [i] da [u] a harshen Hausa.
*Gajeren wasali a tsarin Hausa.
*The Zaria & Kano dialects of spoken Hausa.
*Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa
*Jagoran nazarin tsarin sautin Hausa
* An Introductory Phonology of Hausa.
*Ilimin tsarin sauti na Hausa
*Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare
*Alfiyyar Mu'azu Sani
Farfesa Mu'azu Sani Zaria ya bar mata biyu da 'ya'ya 11 -- mata hudu, maza bakwai da jikoki biyar.