Hadiza Gabon ta ci gasar Africa Films Awards

UZEE CONCEPT

Asalin hoton, UZEE CONCEPT

Bayanan hoto,

Uzee Concept ya yi matukar murna

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani Hadiza Gabon ta lashe kyautar 'yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim a bikin bayar da kyautar Africa Films Awards na shekarar 2016.

Bikin, wanda aka yi ranar Asabar da almuru a birnin London ya kuma karrama Jamilu Yakasai da Uzee Concept.

Wadanda suka hada bikin sun ce Hadiza Gabon na daya daga cikin jaruman Kannywood da suka fi shahara kuma ana yin koyi da ita saboda tana riko da al'adunta da yin shiga mai kyau.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, 'yar wasan ta ce ta sadaukar da kyautar ga magoya bayanta da kuma Ali Nuhu bisa taimakonta da yake yi.

Uzee Concept dai ya lashe kyautar gwarzon mai hada fina-finai na shekarar 2016.

Ali Nuhu da dan majalisar wakilan Najeriya wanda aka dakatar, Abdulmumini Jibrin na cikin wadanda suka halarci bikin.