Pacquiao ya koma fagen dambe

Pacquiao

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pacquiao ya ce mai yuwuwa ya sake fafatawa da Mayweather

Dan damben boksin Manny Pacquiao ya koma fagen dambe inda kuma ya doke zakaran damben Jessie Vargas kana ya lashe gasar WBO a Las Vegas.

A watan Afrilu ne tsohon gwarzon dan damben duniyar na rukuni na takwas din, mai shekara 37, ya bayyana cewa ya daina dambe bayan ya doke Timothy Bradley.

Pacquiao ya zama dan majalisar dattawa a kasarsa Phillipines.

Sai dai ya ce ya koma fagen dambe ne "domin shi ne babban abin na fi so a rayuwata."

Alkalan wasan sun ce ya yi nasara da ci 114-113, 118-109 da kuma 118-109.

Tsohon abokin karawarsa Floyd Mayweather Jr na wurin da ya lashe gasar.

Mayweather ya ce Pacquiao ya yi rawar gani, yana mai jinjina masa bayan an kammala wasan.

Mayweather ne dai ya doke Pacquiao inda ya zama gwarzon dan damben boksin na duniya a watan Mayun shekarar 2015 a fafatawar da ake yi wa lakabi "babban karon-battar wannan zamani".

Pacquiao ya ce shi ne ya gayyaci Mayweather domin halartar wurin damben da ya yi, kuma da aka tambaye shi ko za su sake fafatawa sai ya ce "za mu gani."