Amurka: Ko wa ye zai yi nasara tsakanin Clinton da Trump?

Mista Trump da Misis Clinton
Bayanan hoto,

Kasa da mako guda ya rage a yi zaben Amurka

'Yan takarar shugabancin Amurka na Hillary Clinton da Donald Trump na gab da kammala yakin neman zabe a jihohin da babu wanda kai tsaye zai ce zai lashe kuri'un su.

Hasashe na baya-bayan nan ya nuna Misis Clinton ce ke sahun gaba a yakin da ake yi na shiga fadar White House, inda ta kai ziyara yankunan da a makonni biyun da suka wuce ake zaton za ta kai labari.

Wakiliyar BBC ta ce dukkan bangarorin biyu sun zage dantse dan ganin sun yi nasara a zaben da ke tafe a mako mai kamawa.

Misis Clinton dai ta ta marawa fitaccen mawakin nan bakar fata Jay-Z baya a jihar Ohio dan karfafawa Amurkawa bakar fata gwiwar fitowa don kada kuri'a.

A bangare guda kuma hannayen jarin wasu kamfanonin sun yi matukar faduwa, saboda fargabar da ake kan cewa watakil Donald Trump ne zai yi nasara a zaben da za yi cikin mako mai zuwa.

Hannayen jarin kamfanin S&P sun fadi da kusan kashi 4 cikin 100, amma farashin gwal ya samu tagomashi fiye da makonnin da suka wuce.

Wakilin BBC ya ce masu zuba jarin na fargabar ba su san irin tsarin da Mista Trump zai zo da shi ba matukar ya zama shugaban Amurka.