'Yan Koroya ta Kudu za su yi zanga-zangar kin jini Mis Park

Park Guen-hye
Bayanan hoto,

Aminiyar Mis Park ce ta fara janyo cece-kucen, saboda amfani da kawancen wajen sanya kanta cikin harkokin gwamnati

A Koriya ta Kudu dubban 'yan kasar ne ake sa ran za yi jerin gwano a titunan birnin Seoul tare da bukatar shugaba Park Geun-hye ta yi sauka daga mukamin ta.

Wannan dai zai zamo bore mafi girma da aka taba yi a kasar, wanda 'yan Koriya ta Kudu ke zargin Mis Park da barin aminiyarta da yin katsa landan a harkokin mulkin kasar, ciki har da samun kudade daga kamfanoni wanda hakan ya zabawa dokokin kasar.

A jiya juma'a ne shugaba Park cikin hawaye ta nemi afuwar 'yan kasar, a wani jawabi da aka watsa kai tsaye daga gidan talabijin.

Sai dai Choo Mi-ae jagorar jam'iyyar adawa ta Democratic Party ta ce ba ta yadda da kalaman afuwar Mis Park ba, ta ce jawabin da Park ta yi na kare kai ne kawai, da babu gaskiya a ciki.

Idan har ta na son ci gaba da mulki to ta dakatar da batun nada sabon firaiminista, ta amince da wanda 'yan majalisa suka gabatar.

Sannan ta cire hannun ta a harkokin gwamnati da bai kamata ta tsoma baki a ciki ba.