BH ta kashe wani babban sojin Najeriya

Nigeria soldiers

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya a bakin daga

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.

Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin yaki.

Saboda jarumtarsa ne, a 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin artabun.

Ya ce wasu sojojin hudu kuma sun samu raunuka a harin wanda mayakan kungiyar suka kai a daren Juma'a.

Kanar Kukasheka ya ce cikin makaman da sojojin suka kwace daga wurin mayakan sun hada da babbar bindiga samfurin GPMG, da AK-47 guda bakwai da kuma albarusai da dama.

Asalin hoton, Nigeria Army

Bayanan hoto,

Makaman da sojoji suka kwato daga mayakan Boko Haram

Kakakin sojin ya kuma ce ana ci gaba da aikin kakkabe mayakan Boko Haram din daga yankin.

A 'yan kwanakin nan dai, 'yan bindiga da ake gani mayakan Boko Haram ne sun yi ta yunkurin kai hare-hare a sassan jihar Borno da dama.

Ko a karshen watan Oktoba, sojojin Najeriyar biyar da 'yan sintiri uku da dan kato da gora daya sun rasa rayukansu lokacin da mayakan Boko Haram din suka yi musu kwanton bauna a kauyen Ugundiri dake karamar hukumar Damboa.

Sojoji sha tara kuma da dan kato da gora daya sun sami raunuka a kwanton baunar.