Ba na fargabar zaman gidan kaso— Zuma

South Africa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Jocob Zuma na Afirka ta Kudu

Shugaban Afirka ta Kudu Jocob wanda ake alakantawa da zarge-zargen cin hanci da rashawa, ya ce baya fargabar zaman gidan yari, saboda shekaru goman da ya shafe a kurkuku lokacin da yake mai fafutukar yaki da mulkin wariyar launin fata.

Wannan ne karo na farko da shugaban ya mayar da martani a bainar jama'a, tun bayan da wani binciken cin hanci, ya bada shawarar a binciki shugaban da wasu manyan jami'an gwamnati akan ko sun yi wata hulda wacce bata dace ba da wasu hanshakan 'yan kasuwa 'yan kasar India.

Mista Zuma ya shaida wa dubban magoya bayansa a lardin Kwa-Zulu Natal, cewa lauyoyi da kotuna na kokarin tsawaita muhawara ta demukradiya.

A cikin mako mai zuwa ne ake gani majalisar dokokin kasar za ta gabatar da kudurin rashin bashi goyon baya, koda yake a baya, ya tsallake kudurori biyu na janye goyon bayan da majalisar ke bashi.