Ba ma yin sihiri a fadar shugaban kasa— Geun-hye

South Korea President

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye

An gudanar da zanga-zanga mafi girma a shekaru masu yawa a birnin Seoul na kasar Korea ta Kudu, inda masu zanga-zangar suka bukaci shugabar kasar Park Geun-hye da ta yi murabus.

Wadanda suka shirya ta, sun ce mutane dubu dari biyu ne suka fito aka yi zanga-zangar ta lumana da su, koda yake 'yan sanda sun ce yawan mutanen bai kai haka ba.

Masu zanga-zangar sun nuna damuwa ne akan zarge-zargen da ake yi kan yadda shugabar ta bar wani abokinta na kud-da-kud, wanda bai da mukamin komai a gwamnatin kasar, amma ake yin yadda yake so da wasu manufofin kasar.

A Jiya Juma'a, shugabar ta ba jama'a hakuri, sannan ta musanta zargin cewa an mata asiri ne, ko kuma tana yin tsafi a fadar shugaban kasar.