Somalia: An kai harin kunar bakin wake kusa da majalisar dokoki

Al-Shabab na son fatattakar dakarun wanzar da zaman lafiyar da ke Somalia
Bayanan hoto,

Al-Shabab na son fatattakar dakarun wanzar da zaman lafiyar da ke Somalia

Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan wani jerin gwanon motocin sojoji a kusa da majalisar dokokin Somaliya da ke Mogadishu lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu.

Kafafan yada labaran kasar sun ce adadin wadanda suka rasa rayukansu zai iya zarta haka.

Kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar ta Al-Shabab wadda a baya ta kwace ikon kusan kasar ta Somalia, yanzu ta na son ta fatattaki dakarun wanzar zaman lafiyar da ke kasar.