Haider al-Abadi ya yi kira ga kungiyar IS ta yi saranda

Al-Abadi ya ce IS ta yi saranda
Bayanan hoto,

Al-Abadi ya ce IS ta yi saranda

Firayiministan Iraqi, Haider al-Abadi ya yi kira ga mayakan kungiyar IS a birnin Mosul da su mika wuya.

Lokacin da ya kai wata ziyara a fagen daga kusa da birnin, Mista Abadi ya ce indai mayakan IS din na son rayuwarsu, to wajibi ne su ajiye makamansu.

Dakarun gwamnatin dai sun sami nasarar kara dannawa gabashin birnin na Mosul, kuma a yau Asabar ma, rundunar sojin kasar ta ce dakarunta sun danna cikin garin Hammam al-Alil dake kusa da Mosul din.

A kwanaki biyun da suka gabata, wani sako da aka ce daga wurin shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya fito, ya bukaci mayakan da kada su gudu, kada kuma su ja da baya.