Jami'an tsaro sun janye Trump daga wajen yakin neman zabe

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Trump dai ya ce zai kai yakin neman zaben har a jihohin da jam'iyyar Demokrat ke da karfin gaske.

An janye dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump daga kan dandamalin da yake jawabi yayin yakin neman zabensa a jihar Nevada sakamakon wani firgici da aka samu a wajen.

Jami'an tsaro ne dai suka yi gaba da shi bayan da wani ya yi kururuwa cewa ya ga wani da bindiga a wajen; kodayake da aka bincika ba a ga kowane irin makami ba.

An dai samu rudu tsakanin magoya bayan dan takarar na jam'iyyar Refablika inda har wasu suka nemi wurin gudu saboda kururuwar ta cewa an shigo da bindiga a zauren.

Rudun ya karu lokacin da sojoji suka shigo zauren amma da aka bincika ba a samu kowane irin makami sai aka yi awon gaba da wani mutum wanda ake zargin shi ne ya yi fara yin kururuwar.

Bayan 'yan mintuna Mr. Trump ya dawo zauren idan ya ci gaba da jawabinsa.