An kama mutane 16 da suka buya a jirgi don zuwa Amurka

za a mika mutanen ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin daukar mataki na gaba.
Jami'an sashen bincike da kuma ceto na hukumar kula da tashohin jiragen ruwan Najeriya tare da sojojin ruwa na kasar sun kama wasu mutane 16 da suka shiga kuma suna buya a cikin wani jirgin ruwa mai niyyar zuwa Amurka.
An kama mutanen da suka hada da dan kasar Liberia guda ne a kusa da gabar ruwan babban birnin kasuwancin kasar wato Legas.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun hukumar ta tashoshin jirage ruwa wato NIMASA, Hajiya Lami Tumaka, ta ce an kama mutanen ne bayan da matukin jirgin ya aike da wani sakon neman dauki zuwa ga cibiyar tsara bincike da kuma aikin ceto ta hukumar wadda ita kuwa ta sanar da sojan ruwan Najeriya.
Ta ce daya daga cikinsu ya samu rauni a kafada lokacin da yake kokarin tserewa amma jami'an aikin ceto na hukumar sun garzaya da zuwa asibiti domin yi masa magani, yayin da jami'an sojin ruwan suka yi awon gaba da sauran mutanen 15 domin daukar bayanansu da kuma mika su ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike.
Matuka jirgin na MV Colombia River wanda aka yi wa rijista a tsibirin Hong Kong, sun ce da farko sun zaci cewa 'yan fashin teku ne suka kawo musu farmaki, amma binciken farko-farko ya nuna cewa mutanen masu kutse ne kawai da suka so bin jirgin zuwa kasar Amurka domin neman abin yi.