Hikayata 2016: Labarin Sansanin 'Yan Gudun Hijira da ya yi na daya

Hikayata 2016: Labarin Sansanin 'Yan Gudun Hijira da ya yi na daya

A wannan makon muke fara karanto muku gajerun labarai uku da suka yi nasarar lashe gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla da ma wasu 12 da suka cancanci yabo.

Alkalan gasar ne dai suka zabo wadannan labaran daga cikin 21 da suka tantance, bayan sun fitar da ukun da suka yi fice.

A yau za mu fara ne da labarin da ya zo na daya, wato Sansanin 'Yan Gudun Hijira, wanda za ku ji shi daga bakin wadda ta rubuta shi, A'isha Muhammad Sabitu: