Dole Manchester City ta sauya wasa - Guardiola

Aguero ya yi takaicin rasa makinsu.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Aguero ya yi takaicin rasa makinsu.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce dole ne su inganta wasan da suke yi a kusa da ragarsu domin hana yin asarar maki a gasar Premier.

City da Middlesbrough sun raba maki daya da daya a tsakaninsu, bayan da suka tashi wasan da ci1-1 a fafatwar da suka yi a Ettihad.

Hakan ya bai wa Chelsea damar yin gaba da su inda ta zama ta daya a kan tebirin gasar.

'Yan wasan City sun rike kwallo har kashi 71 a wasan, sannan suka dirka kwallon sau 25 sabanin Middlesbrough da suka dirka kwallo sau biyar, amma duk da haka sun gaza yin nasara a karo na uku a jere a gidansu.

Guardiola ya ce, "Muna bukatar samun daidaito, amma ba a samun hakan a kusa da ragarmu."

City ce ta fara cin kwallo ta hannu Sergio Aguero -- wadda ta zame kwallonsa ta 150 da ya ci wa kungiyar tun lokacin da ya fara taka mata leda.

Sai dai Middlesbrough ta farke ta hannun De Roon ana daf da tashi daga wasan.