Iska mai gurbata muhalli ta sa an kulle makarantu a Delhi

Mummunar iska ta mamaye kofar shiga Delhi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mummunar iska ta mamaye kofar shiga Delhi

Ministan Delhi na kasar India ya sa an kulle dukkan makarantun birnin tsawon kwana uku a yayin da mazauna birnin ke fama da iska mai gurbata muhalli.

Arvind Kejriwal ya bayyana hakan ne bayan wani taron gaggawa da ya gudanar da masu ruwa da tsaki, yana mai shan alwashin shawo kan matsalar.

Yanzu haka dai an dakatar da dukkan ayyukan gine-gine da rushe-rushe a birnin har kwana biyar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Bikin Dewali ya ta'azzara mummunan yanayin da ake ciki aDelhi

Za a feffesa ruwa a kan manyan titunan birnin domin kwantar da kurar da ke damun mutane.

Mr Kejriwal ya bayar da shawara ga mazauna binrin na Delhi da su yi zamansu a cikin gidajensu kana ma'aikata su yi ayyukansu a gida idan da dama.

Kazalika gwamnati ta sanar da cewa za a kashe wutar da ake kunnawa a kamfanonin fada dutse, sannan a rufe tashar samar da ma'adinin kwal da ke Badarpur.

Tun ranar Asabar ne dai aka rufe makarantu 1,800 na kwaryar birnin saboda iska mai gurbata muhalli.