Za a kaddamar da yakin kwato Raqqa

Asalin hoton, Reuters
An gargadi farar hular da ke yankin
Wasu mayakan Kurdawa da Larabawa, wadanda Amurka ke goya wa baya sun ce za su kaddamar da yakin kwato Raqqa, inda aka ce shi ne babban birnin da ke hannun kungiyar IS a Syria.
Mayakan kungiyar Syria Democratic Forces (SDF) sun ce gamayyar rundunar da Amurka ke jagoranta ce za ta taimaka musu da kai hare-hare ta sama nan da sa'oi kadan masu zuwa.
Sun gargadi farar hula da ke birnin da su fice daga unguwannin da mayakan IS suke.
Mayakan na Kurdawa da Larabawa dai sun mamaye unguwanni da dama na arewacin birnin.
Za su kaddamar da hare-haren ne a daidai lokacin da dakarun Iraqi wadanda Amurkawa ke goyon baya ke ci gaba da kokarin korar mayakan IS daga birnin Mosul inda suka fi karfi.