Wanene Laftanar Kanar Muh'd Abu-Ali?

  • Haruna Shehu Mjos
  • BBC Hausa
nigerian army

Asalin hoton, Nigerian army

Bayanan hoto,

Lokacin da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Burutai ke yi wa Laftanar kanar Abu-Ali karin girma

Labarin rasuwar kwamandan rundunar sojin Najeriya ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali, shi ne kusan batun da yafi kowanne jan hankalin ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya a ranakun karshen mako.

Laftanar Kanar Abu-Ali yana cikin sojoji biyar da suka rasa rayukansu a daren Juma'a, yayin bata kashi da mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai hari kan wani barikin soji dake Mallam Fatori a jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya.

Rundunar sojin Najeriyar ta sha bayyana dakarunta da su ke rasa rayukansu a rikicin Boko Haram, a matsayin jarumai, wadanda suka sadaukar da rayukansu don kare rayukan sauran jama'ar kasar.

Sai dai a wurin hukumomin sojin Najeriyar, jaruntar Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali ta daban ce. Hakan ne ma yasa ya samu karin girma na daban a cikin yakin da ake yi da Boko Haram.

A watan Satumban 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali

Wace irin jarumta ya nuna?

A cikin sanarwar sojin kasar wacce ta tabbatar da kashe Laftanar Kanar Abu-Ali, kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka ya bayyana shi a matsayin sojan da ya nuna jarunta ta daban.

Hakanne a cewar shi, ya sa aka yi mushi karin girma tun kafin ya cika shekarun samun karin girman.

A wata hira da Bilkisu Babangida, Kanar Kukasheka ya ce idan ana neman jarumin soja, to in aka samu Laftanar Kanar Abu-Ali, babu sauran magana kuma:

Bayanan sauti

Kakakin Sojin kasa na Najeriya, Kanar Kukasheka

Masu sharhi da marubuta da dama a Najeriyar sun ce mariganyi Laftanar Kanar Abu-Ali, ya yi suna ne a yakin da dakarun kasar ke ci gaba da yi na kawar da kungiyar Boko Haram.

A wani rubutu na girmamawa ga mamacin, Hamza Idris, tsohon ma'aikacin jaridar Daily Trust a arewa maso gabashin Najeriya, ya bayyana shi a matsayin mutun mai zuciya irin ta zaki, sarkin daji wanda ba ya gudu, ba ya ja da baya har zuwa lokacin da rayuwarshi ta kare.

A cewar Idris, mutanen jihar Borno, wadanda su ne suka fi shan wahalar rikicin Boko Haram, su ne za su fi kowa sanin wanene Laftanar Kanar Abu-Ali, saboda a cewarshi, Laftanar Kanar Abu-Ali, ya na gaba-gaba a cikin sojojin da suka sarrafa manyan makaman da aka girke a arewa maso gabashin Najeriya domin yaki da Boko Haram.

Tun a watan Yunin wannan shekara, lokacin da ba wanda ya kawo cewa ta Allah za ta faru da Laftanar Kanar Abu-Ali a wannan lokaci, Editan jaridar TheCable, wacce ake wallafa wa a intanet, Fisayo Soyombo ya yi rubutu na jinjinawa jarumtar sojan.

Soyombo ya ce kamar yadda rahotanni suka nuna, jaruntar da Laftanar Kanar Abu-Ali ya nuna wajen sarrafa tankokin yaki, ita ta taimaka sojoji suka kwato garin Baga da Gamboru-Ngala daga hannun kungiyar Boko Haram.

Wasu sojoji da suka yi aiki a karkashinsa, sun shaida wa BBC cewa samun jagora irin Laftanar Kanar Abu-Ali ya na da wuya, domin shi mutun ne mai karfafa gwiwar na kasa da shi, da kula da bukatunsu, da shiga gaba a duk inda aka dosa.

Asalin hoton, Nigerian army

Bayanan hoto,

Mariganyi Laftanar Kanar Muhammad Abu-Ali a tsakiya

Marigayin dan asalin jihar Kogi a tsakiyar Najeriya ne, kuma da ne ga basaraken masaraunar Nge, Birgediya Janar Abu Ali mai ritaya.

Mahaifin na shi ma jarumin soja ne wanda ya taba zama gwamnan jihar Bauchi a zamanin mulkin soji.