Hare-haren IS sun halaka mutane 21 a Iraki

Asalin hoton, EPA
Daya daga cikin wuraren da aka kai harin
Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai wasu hare-haren kunar bakin wake biyu a biranen Tikrit da Samarra na Iraki, inda ta kashe akalla mutane 21.
An kai dukkan hare-haren ne ta yin amfani da motocin daukar marasa lafiya da aka shake su da bama-bamai.
An tayar da daya daga cikin bama-baman ne a kan layin motocin dake jira a bincike su a wurin duba ababen hawa a Tikrit.
Shi kuma harin na Samarra, an kai shi ne a wurin da ake ajiye motoci da masu ibada 'yan shi'a ke amfani da shi.
Jami'ai sun ce 10 daga cikin wadanda suka mutun 'yan kasar Iran ne.