An gano kokunan kan mutane 40 a Bangladesh

skulls
Bayanan hoto,

Kasusuwan mutane

'Yan sanda a Bangladesh sun gano kokunan kan mutun guda 40, da wasu kasusuwan mutane a wani gida a Dhaka, babban birnin kasar.

'Yan sandan sun kuma kama wani dalibi dake karatun aikin likita.

Wani jami'in 'yan sandan ya shaidawa BBC cewa dalibin da aka kama, ya amsa cewa yana sayar da kasusuwan mutanen ne ga daliban dake karatun aikin likita akan kudi dala 450 kowanne daya.

Ana gani dalibin yana tono kasusuwan mutanen ne a makabartu a wajen birnin, sannan ya wanke su da sinadarai da sauran kayan aiki.

'Yan sandan yanzu, suna na kokarin gano sauran mutanen da yake sana'ar tare da su.