Hillary Clinton ba ta da laifi in ji hukumar FBI

FBI ta ce ba a samu Hillary da laifin komai ba
Bayanan hoto,

FBI ta ce ba a samu Hillary da laifin komai ba

Daraktan hukumar FBI ya ce bayan nazari a kan sabbin sakonnin emails din da aka gano na Hillary Clinton a lokacin da ta ke matsayin sakatariyar harkokin wajen Amurka, hukumar na nan kan ra'ayinta na farko cewa ba za a gurfanar da ita gaban kuliya ba.

Kwanaki biyu kafin zaben shugaban kasar da za a yi, James Comey ya aike da wasika ga majalisar dokokin kasar in da ya ce hukumar ta FBI ba ta canja matsayarta ta watannin baya ba cewa Mrs Clinton ba tayi laifi ba wajen ta'ammali da bayanan sirri.

A makon da ya gabata ne dai yakin neman zaben Mrs Clinton ya shiga rudani bayan da Mr Comey ya ce jami'an hukumar sa za su sake nazari a kan sakonnin ta na email.

Jam'iyyar Democrats ta ce wannan sanarwa ta zo a makare ta yadda hukumar FBI din ba zata iya goge bata sunan da ta yiwa Mrs Clinton ba.