Jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin gurguzu a Bulgaria ta yi zarra

Ana kyautata zaton Rumen Radev ya samu kaso daya bisa hudu na kuri'un da aka kada

Asalin hoton, Picture- alliances

Bayanan hoto,

Ana kyautata zaton Rumen Radev ya samu kaso daya bisa hudu na kuri'un da aka kada

Sakamakon jin ra'ayin masu zabe a Bulgari ya nuna cewa jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin gurguzu wanda dan takararta ke son kulla dangantaka da Rasha ta samu nasara a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka yi.

Ana kyautata zaton Rumen Radev ya samu kaso daya bisa hudu na kuri'un da aka kada, inda hakan ya nuna cewa ya samu nasara a kan abokiyar takararsa Tsetska Tsacheva ta jam'iyyar da ke mulki a kasar.

Idan har aka tabbatar da sakamakon zaben, to hakan ya nuna cewa firayim minista Bokyo Borisov ya samu koma baya.

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin manyan 'yan takara biyu.