Clinton: Trump ya zargi FBI da taimaka wa magudi

Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wani mashawarcinsa, Newt Gingrich, ya ce Mr Comey ya sha matsin lamba ne mai girman gaske daga 'yan siyasa

Donald Trump ya soki hukumar FBI saboda cewar da ta yi Hillary Clinton ba za ta gurfana gaban kotu ba kan sabbin sakonnin e-mail dinta da hukumar ke bincike a kai.

Mr Trump ya shaidawa wani gangamin yakin neman zabensa a jihar Michigan cewa hukumar ba za ta iya yin nazari kan sakonni e-mail 650,000 ba a cikin kwannaki takwas kawai ba.

Sannan ya kara da cewa Mrs Clinton na samun kariya ne daga gwamnatin da ke goyon bayan magudi.

Kalaman nasa dai sun zo ne jim kadan bayan shugaban hukumar ta FBI, James Comey ya aike da wata wasika zuwa ga majalisar dokokin kasar cewa matsayin hukumarsa bai canza ba daga wanda ta cimma a watan Yuli cewa ba a samu wani abin zargi ba a sakonnin na e-mail.

''Mun ga wasikar da Daraktan FBI Comey ya aike wa majalisar dokoki.

Mun ji dadi da cewa ya kara tabbatar da matsayar da suka cimma a watan Yuli. Muna farin ciki cewa an warware wannan matsalar.'' In ji mai magana da yawun ofishin kamfe din Mrs Clinton, Jennifer Palmeiri.