Nigeria ta aike da 'yan sanda mata sansanonin 'yan gudun hijira

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, AF

Bayanan hoto,

Kungiyar 'yan Boko Haram sun lalata kauyuka da dama a arewa masogabas

An aike da 'yan sanda mata 100 a sansanonin 'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Najeriya ta dauki matakin ne bayan wata kungiyar masu fafutuka ta zargin jama'ian tsaro maza da cin zarafin mata da kananan yara.

Shugaban 'yan sanda na jihar, Damian Chukwu ya ce an dauki matakin ne domin karfafa gwiwar dubban mata da kananan yara mata da ke sansanonin.

Ya kara da cewa " muna ganin cewa matan ba za su saki jiki suyi magana da maza ba, amma zasu samu kwarin gwiwar bayyana wa 'yan sanda mata idan har ya kasance zargin da ake yi gaskiya ne".

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya bukaci a yi bincike a kan batun ne bayan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human rights Watch ta ce ta yi magana da mata 43, wadanda jami'an tsaro ko kungiyar 'yan banga suka yi wa fyade ko suka ci zarafinsu.