Waye zai zama sabon shugaban Amurka?

Masu kada kuri'a a Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'a sun fito sosai domin kada kuri'unsu

Al'ummar Amurka na kada kuri'a domin zaben sabon shugaba bayan yakin neman zabe mafi zafi da aka taba yi a tarihin kasar.

Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara kada kuri'a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun kada kuri'unsu.

Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada kuri'unsu a mazabu daban-daban a birnin New York.

An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da ke nuna yadda jama'a suka fito sosai.

Wasu wuraren kada kuri'ar sun samu matsalolin na'ura, abin da ya haifar da jinkiri.

Za a fara samun sakamako a cikin daren ranar Laraba da misalin karfe 04:00 na safe.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Clinton dai na gaban Trump da maki hudu kacal a kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wanda ya fi farin jini

Duka 'yan takarar sun yi gangamin yakin neman zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.

Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta zaben gama-gari.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan asalin Latin Amurka masu amfani da yaren Spaniya, wadanda ke goyon bayan Hillary Clinto, sun fito sosai.

Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye kasar domin neman kuri'un jama'a a 'yan kwanakin da suka gabata.